On Air Now

Off Air

Midnight - 5:00am

Kungiyoyin ASUU Da ASUP Sunce Babu Tabbas Wajen Aiwatar Da Dokar Bada Lamunin Karatu

TINUBU

Kungiyar malaman jami’o’I ta kasa ASUU, ta bayyana dokar bada lamunin karatu ga daliban manyan makarantu a kasar nan, da shugaban kasa Bola Tinubu ya sanyawa hannu a jiya, matsayin nuna banbanci tsakanin ‘ya’yan masu hannu da shuni da kuma ‘ya’yan talakawa.

Da yake mayar da martani  kan dokar  da  shugaban kasa  ya saka wa  hannu, shugaban kungiyar ASUU na kasa, Farfesa Emmanuel Osodeke, ya ce idan har da gaske an samar da dokar ne domin amfanin  yaran da iyayensu ke samun samun abunda bai wuce naira  dubu  500  a  shekara  ba, hakan na nufin daliban da iyayensu ke samun  fiye  da wannan kudi a shekara,  ba zasu ci gajiyar tsarin ba.

Bugu da kari shima  Shugaban Kungiyar Malaman Makarantun Kimiyya ta Kasa, Anderson Ezeibe, ya ce abune  mai wahalar gaske  yadda aka dora tsarin kan cewar  daliban  da suka karbi  bashin,su mayar da kudin bayan shekara biyu da kammala aikin hidimtawa kasa.

A cewarsa,  Ba lallai ba ne  daliban da suka karbi bashin  su samu aikin yi  a  shekara biyu  bayan sun kammala aikin hidimtawa kasa.