On Air Now

ZANGON DARE

8:00pm - Midnight

Kungiyoyin Fararen Hula sun Nemi a Dakatar da Gangamin Siyasa, Kafa Dokar Hana Yaɗuwar Makamai a Kano

Haɗakar wasu ƙungiyoyin fararen hula a Jihar Kano dake rajin tabbatar da siyasa mai tsafta ta yi kira da a dakatar da duk wani gangamin siyasa gabanin babban zaɓen shekarar 2027, tana mai gargadin cewa ƙaruwar rikice-rikicen siyasa da ayyukan 'yan daba da kuma yaɗuwar makamai na barazana ga rayuka, dukiyoyi da kuma dimokuraɗiyya.

Rahoto: Nura Haruna Mudi

Yayin wani taron manema labarai, Sakataren hadakar kungiyoyin Auwal Shu'aibu, ya buƙaci Gwamnatin Jihar Kano da kuma Majalisar Dokoki da su gaggauta samar da dokokin da za su daƙile ƙerawa da mallaka ba bisa ka'ida ba da yaɗuwar makamai, yana mai cewa irin waɗannan makamai na ƙara rura wutar rikicin siyasa a jihar.

Auwal Shu'aibu ya yi zargin cewa 'yan siyasa daga jam'iyyu daban-daban na ci gaba da ɗaukar nauyin, samar da makamai ga 'yan daba da kuma amfani da su wajen gudanar da harkokin siyasa, al-amarin da ya ce na haddasa kashe-kashe da tashin hankali a sassa daban-daban na Kano.

Ƙungiyar ta ambaci rikice-rikicen da suka yi sanadin rasa rayuka a yankunan Koki, Kasuwar Mayanka (Abattoir), Hotoro, Unguwa Uku, Dorayi Karama da kuma kan titin Rimin Kebe da ke bayan ofishin WAEC, tare da tunatar da kisan wani jami'in ɗan sanda da ke aiki a  Hotoro sakamakon arangama tsakanin 'yan daba.

Ta ce hakan na nuna cewa matsalar ta shafi fararen hula da jami'an tsaro baki ɗaya.

Ƙungiyar ta kuma bayyana cewa akwai kashe-kashe da dama da ke da alaƙa da rikicin siyasa da ba a bayar da rahotonsu ba ko kuma ba a yi cikakken bincike a kansu ba, al-amarin da ya haifar da fargaba a tsakanin al'umma tare da kawo cikas ga kasuwanci da zaman lafiya.

Sai dai ƙungiyar ta yaba wa Gwamna Abba Kabir Yusuf kan matakan da yake ɗauka wajen inganta tsaro ƙarƙashin manufar Kano First Agenda, amma ta ce har yanzu akwai buƙatar ƙarin matakai masu tsauri domin murƙushe 'yan daba da kuma hukunta masu ɗaukar nauyinsu.

Daga cikin buƙatun da ƙungiyar ta gabatar akwai dakatar da duk wani gangamin siyasa har sai an samar da ingantaccen tsarin tsaro, gudanar da bincike mai zaman kansa kan kashe-kashen da suka shafi siyasa, ƙarfafa ayyukan jami'an tsaro a wuraren da rikice-rikice suka fi kamari, samar da ayyukan yi da horas da matasa, da kuma kafa kwamitin zaman lafiya da zai haɗa ƙungiyoyin fararen hula, shugabannin addinai, na gargajiya da jam'iyyun siyasa domin sa ido da sasanta rikice-rikice.

A matsayin madadin gangamin siyasa masu cunkoso, ƙungiyar ta ba da shawarar gudanar da tarukan tattaunawa da al'umma da shirye-shiryen Radiyo da talabijin da yaƙin neman zaɓe ta kafafen sada zumunta da ziyartar al'umma gida-gida da tarukan unguwanni da kuma tarukan manema labarai.

A ƙarshe, ƙungiyar ta yi kira ga Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) da hukumomin tsaro da kuma ƙasashen duniya da su sa ido kan halin da ake ciki a Kano, tana mai jaddada cewa babu wata buƙatar siyasa da ta fi darajar rayuwar ɗan Kano ko guda ɗaya ne.

Comments

Add a comment

Log in to the club or enter your details below.

A Biyo Mu a Shafukan Sada Zumunta

Today's Weather

  • Kano

    Sunny intervals

    High: 34°C | Low: 23°C