On Air Now

ZANGON DARE

8:00pm - Midnight

Kungiyoyin Kwadago Sun Baiwa Gwamnoni Wa'din Mako Biyu Domin Fara Biyan Karin Albashi Na Dubu 35

NLC

Gamaiyyar kungiyoyin kwadagon kasar nan sun baiwa gwamnonin jihohi wa’adin makwanni biyu dasu fara yin aiki da yarjejeniyar da suka kulla da gwamnatin tarayya na yiwa ma’aikata Karin naira dubu 35 a albashinsu.

Wannan dai na daya  daga cikin alkawuran da aka kulla tsakanin gwamnatin tarayya  da kungiyoyin kwadagon.

Shugabannin kungiyoyin kwadagon a matakin jihohin wadanda  suka  bada  wannan wa’adi a jiya  Talata, Sunce  sun rubutawa  gwamnonin  wasika kan tsare-tsaren aiwatar da Karin albashin na wucin gadi wanda  za’a yi aiki da shi  tun bayan janye tallafin mai.

Da yake tabbatar da daukar matakin, Shugaban kungiyar kwadago  ta NLC reshen jihar Kano,  Kwamared  Kabiru Inuwa , Y ace  sun aikewa  da gwamnati  jihar kano sakon nasu, kuma a yanzu suna dakon suga  matakin da zata dauka, tare da fatan  gwamnati  zata yi abunda  ya dace  kafin karewar wa’adin da suka bayar.