On Air Now

ZANGON BARKA DA SAFIYA

5:00am - 10:00am

Kungiyoyin Kwadago Sun Fara Yajin Aikin Gargadi

NLC

Kungiyar kwadago ta kasa ta lashi takobin tsayar da dukkanin wasu harkoki a kasar nan cak , a yayin da zata fara yajin aikin gargadi na tsawon kwanaki biyu a fadin kasar nan daga yau, a wani mataki na nuna damuwa kan halin matsin rayuwa da jama’ar kasa suka samu kansu a ciki, tun bayan janye tallafin man fetir.

Masu ruwa  da tsaki a bangaren tattalin arzikin kasa, da  suka hada da Bankuna da  kungiyoyin farar hula da  kungiyoyin ma’aikata  na goyon bayan yajin aikin da za’a soma daga yau,  a kokarinsu na ganin  an magance  matsalolin da tattalin arzikin kasa  ya samu kansa a ciki.

Ma’aikatan bankuna  da kungiya kwararrun ma’aikata a bangaren gudanar da harkokin kudi sun yi alkawarin  rufe  wuraren aiyukansu daga yau.

Wata sanarawa  da  babban sakatarensu, Mohammed  Sheika ya fitar, Ta tabbatar da cewar zasu shiga yajin aikin,  inda  suka ce akwai bukatar jawo hankalin  gwamnatin tarayya kan halin da  ‘yan kasa  ke ciki.

Nan kuma, Shugabancin kungiyar kwadago ta kasa, NLC, Ya kauracewa taron da ministan kwadago Simon Lalong ya shirya, da zummar  ganin an dakile  shirin tafiya  yajin aiki na tsawon kwanaki biyu da kungiyar zata  fara daga Yau.

Rahotanni sun baiyana cewar  shugaban kungiyar kwadago  ta TUC, Festus Osifo ne kadai  ya halarci zaman wanda aka fara da karfe 5 da rabi da minti biyu na yammacin yau.

An yi  ganawar ne  cikin sirri, A yayin da ministan kwadagon ya roki yan Jarida  dasu temaka  su  bar wajen taron, domin kyale masu ruwa da tsaki su tattauna  kan muhimman abubuwan da aka sanya gaba.

A ranar juma’a data gabata ce, Kungiyar kwadagon ta aiyana tafiya yajin aikin gargadi na tsawon kwanaki biyu farawa daga ranar  Talatar nan,  sakamakon halin tsadar rayuwa  da  jama’a suke  ciki.