On Air Now

ZANGON RANA

10:00am - 3:00pm

Kungiyoyin Kwadago Sun Janye Yajin Aiki

Shugabancin gamaiyyar kungiyar kwadago ta kasa ya janye yajin aikin sai Baba ta gani da kungiyar ta fara a fadin kasa daga ranar Talatar data gabata, a wani mataki na nuna borenta kan cin zarafin da aka yiwa shugaban kungiyar kwadago na kasa NLC, Kwamared Joe Ajaero a jihar Imo.

A daren jiya ne kungiyar ta sanar da janye  yajin aikin bayan wata ganawa da  mai baiwa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro, Malam Nuhu Ribadu, Wanda  ya tabbatar da cewar  an kama mutane biyu da ake da zargi  da cin zalin  shugaban kungiyar kwadagon na kasa, tare da rokonsu  dasu janye  yajin aikin.

Babban  sakataren gamaiyyar kungiyoyin ma’aikata ta kasa, Kwamared  Sikiru  Waheed  ne  ya tabbatar da janye yajin aikin  na sai Baba  ta gani ga manema Labarai.

Kwamared  Waheed  ya jinjinawa  Ma’aikata  saboda  jajircewar da suka nuna wajen ganin  yajin aikin ya tabbata cikin nasara, tare da umartarsu  da su koma bakin aiki  daga  yau  Alhamis.