On Air Now

ZANGON RANA

10:00am - 3:00pm

Kungiyoyin Kwadago Sunce Gwamnatin Tarayya Ta Yaudare Su Kan Karin Albashi Na Naira Dubu 35

NLC

Gamaiyyar kungiyoyin kwadago a kasar nan sunga baiken gwamnatin tarayya kan rashin cigaba a biyan ma’aikata karin albashi na wucin gadi na naira dubu 35 da aka yi masu, sakamakon janye tallafin mai da aka yi.

A jiya ne ma’aikatan gwamnatin tarayya  suka tabbatar da cewar, gwamnatin ta yi masu karin  naira  dubu 35 ne sau  daya kadai a albashinsu na watan Satumba, sabanin alkawarin da gwamnatin tarayya  ta yi, na cewar  za’a cigaba da basu karin har zuwa lokacin  za’a bullo  da sabon tsarin biyan albashi mafi kankanta.

Shugaban sashin yada labarai na kungiyar kwadago ta kasa, Benson Upah ya baiyana matakin a matsayin na yaudara wanda kuma ba zasu lamunta ba, inda y ace  kungiyar zata dauki mataki  batare da bata lokaci ba.

To sai dai kakakin  ofishin  babban akanta na kasa,  Bawa Mokwa ya kawar da fargabar da ma’aikatan suka nuna, inda  ya ce  a yanzu haka shirye-shirye  sunyi nisa  domin tabbatar da ma’aikatan sun karbi karbin albashin na wucin gadi  da aka yi masu.