On Air Now

Off Air

Midnight - 5:00am

Kuri'ar Jihar Rivers Jam'iyyar APC Kawai Ke Bukata Daga Gwamna Wike Ba Tallafi Ba - Gwamna Umahi

Gwamna Dave Umahi na Jahar Ebonyi ya roki gwamnan jahar Rivers Nyesom Wike da ya manta da batun bada tallafi na yakin neman zabe ga jam’iyyar APC maimakon hakan ya samrwa dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar, Bola Tinubu kuri’u masu yawa a jihar.

Ya ce APC ba ta bukatar tallafin kayan aiki sai dai kuri'u  daga jihar Rivers.

Umahi ya bayyana haka ne a ranar Talata a yayin kaddamar da wani titi a karamar hukumar Emohua ta  jihar Rivers.

Idan dai za a iya tunawa Wike ya yi alkawarin baiwa dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar NNPP, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso da takwaran sa na jam’iyyar Labour, Peter Obi tallafi ga yakin neman zabensu a jihar.

 Sai dai Gwamna Umah ya nemi a ba shi wani abu mai sauki, inda ya ce abin da jam’iyya mai mulki ke bukata shi ne goyon bayan jahar Rivers ta fuskar kuri’u.

More from Labarai