On Air Now

ZANGON DARE

8:00pm - Midnight

Kuyi Hakuri Da Yadda Za'a Yi Rabon Mukaman Majalisar Dokoki Ta Kasa Inji APC

ABDULLAHI ADAMU

Shugaban jam’iyyar APC na kasa, Abdullahi Adamu ya bukaci ‘yan Najeriya da su yi hakuri da jam’iyyar game da yadda za’a yi rabon mukaman shugabancin majalisar dokokin ta kasa a tsakanin shiyyoyin kasar nan.

Adamu ya bayyana haka ne, jim kadan bayan wata ganawar sirri da  ya  yi tsakaninsa  da  zababben shugaban kasa, Bola Tinubu da wasu shugabannin jam’iyyar  da  sauran masu ruwa da tsaki a gidan da zababben shugaban kasa  ke zama a Abuja.

Sanata Adamu ya bukaci ‘yan Najeriya su yi hakuri da jam’iyyar  kan yadda  zata yi fasalin shugabancin majalisar dokoki ta kasa.

Sauran wadanda suka halaci taron  sun  hada da shugaban majalisar dattawa   sanata  Ahmad Lawan da  Mataimakin shugaban majalisar dattawa, OvieOmo-Agege da  kakakin majalisar  wakilai  Femi Gbajabiamila sai kuma  Kakakin majalisar  dokokin jihar  Kaduna Yusuf Zailani.