On Air Now

ZANGON BARKA DA SAFIYA

5:00am - 10:00am

Kwale-Kwale Ya Kife Da Mutane 100 A Jihar Naija

kwale-kwale

A jiya ne, Wani kwale-kwale dauke da fasinjoji kimanin 100 ya kife a karamar hukumar Borgu dake jihar Naija.

Mutane da dama ne suka yi bace biyo bayan faruwar  hadarin, kamar yadda shugaban hukumar bada agajin gaggawa  ta jihar Naija  Abdullahi Baba Arah, ya tabbatar.

Ya fadawa manema labarai a daren jiya cewar, har zuwa  yanzu  babu cikakken bayanin adadin mutanen  da suka mutu.

Abdullahi Baba ya kara da cewar, Kwale-kwalen ya ta so ne  daga  mazabar Dugga Mashaya  a karamar hukumar Borgu ta jihar Naija, inda  yake kan hanyarsa ta zuwa  Kasuwar Wara dake  jihar Kebbi, dauke da fasinjoji da kuma kayayyaki kamar su Hatsi da Rake.