On Air Now

ZANGON MARAICEN LAHADI

6:00pm - Midnight

Kwamishinan 'Yansandan Jihar Kano Ya Bada Umarnin Kamo Matashin Da Ya Halaka Mahaifiyarsa Da Wuka

Kwamishinan ‘yan sandan jihar Kano, Mohammed Usaini, ya ba da umarnin kamo wani mai matashi mai suna Ibrahim Musa dan shekaru 22 a duniya , wanda ake zargin ya halaka mahaifiyarsa mai suna Hajara Mohammed mai shekaru 50 a duniya, Ta hanyar daba mata wuka.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Kano, SP Abdullahi Haruna-Kiyawa   shi ne ya bayyana haka  ta  cikin  wata sanarwa da ya fitar a  nan  Kano.

Ya kara da cewa, An garzaya  da matar  zuwa  Asibitin koyarwa  na Mohammed Abdullahi Wase da ke  nan  Kano, inda  a nan  ne kuma  wani Likita ya tabbatar da mutuwar ta.

Ya kuma baiyana cewar  an samu wata wuka dauke da jini a  jikinta   wadda ake zargin  da ita matashin ya yi amfani wajen aikata danyen aikin.

Kakakin rundunar  yansandan jihar  Kano ya  ce  a yanzu haka kwararrun jami’ansu  na kan  neman  matashin ruwa  a jallo.