On Air Now

ZANGON MARAICE

3:00pm - 8:00pm

Kwamitin Sulhu Na Jam'iyyar PDP Zai Gana Da Gwamna Nyesom Wike.

ATIKU DA WIKE

kwamitin amintattu na jam’iyyar PDP ya kafa kwamitin sulhu domin ganawa da Gwamna Nyesom Wike na jihar Rivers kan faduwa zaben fidda gwani na jam’iyyar da kuma rikicin da ya biyo bayan zaben na fitar da gwani.

Kwamitin dai zai kasance karkashin dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar kuma tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, kuma yana da gwamnonin PDP 13 a matsayin mambobi.

Shugaban kwamitin amintattu na jam’iyyar, Sanata Walid Jibril shine ya bayyana hakan a wata sanarwa  da ya fitar ranar Lahadi.

Jibril ya ce za’a kaiwa Wike ziyarar da zarar Atiku da Shugaban Jam’iyyar PDP na kasa, Iyorchia Ayu sun dawo kasarnan daga balaguro da sukayi zuwa ketare…