On Air Now

Off Air

Midnight - Noon

Kwana Biyar Gabanin Rufe Kofa Ga Mahajjatan Bana Sama Da Rabin Maniyatan Najeriya Na Zaman Jiran Tsammani

Kwanaki kadan da fara aikin hajjin bana, ana fargabar cewa dubban maniyatan Najeriya na iya rasa aikin hajjin, kamar yadda wani rahoton jaridar Daily Trust ya nuna.

Ya zuwa lokacin gabatar da wannan rahoto, an kwashe kasa da rabin maniyatan kasarnan dubu 43 daga Najeriya.

Alkaluman da hukumar aikin hajji ta kasa NAHCON ta fitar, sun nuna anyi jigilar  maniyata dubu 19 da 764 daga jihohi 23.

Jihohin Kano da Kaduna da ke da yawan maniyata har yanzu da yawa daga cikin masu shirin zuwa aikin hajjin  suna jiran tashin jiragen su.

Ya zuwa jiya, an kwashe maniyatan Kaduna dubu 1 da 593 daga cikin dubu 2 da 491.

Yayin da a Kano, maniyyata 399 ne kacal aka kai kasar saudiyya daga cikin dubu 2 da 229 da aka warewa jihar.

 Hukumomin Saudiyya sun ce dole ne dukkan maniyyatan su isa zuwa ranar 3 ga watan Yuli.