On Air Now

ZANGON DARE

8:00pm - Midnight

Kwankwasiyya ta yi Zargin Take Hakkokin Mambobinta Dake Tsare a Hannun Jami'an Tsaro

Magoya bayan darikar siyasa ta Kwankwasiyya sun shigar da ƙara a gaban Hukumar Kula da Ayyukan Shari’a ta Jihar Kano, da Babbar Alkaliyar Jihar Kano, Mai Shari’a Dije Abdu Aboki, da kuma Babban Khadi, Dakta Tijjani Yakasai, kan zargin tsare wasu mambobinsu biyu da kuma tsauraran sharuɗɗan beli da aka gindaya musu.

Da yake magana da manema labarai jim kaɗan bayan shigar da ƙarar, Dakta Yusuf Ibrahim Kofar Mata ya zargi Alƙali Muhammad Sharama Abdulkadir da sanya tsauraran sharuɗɗan beli, ciki har da gabatar da Babban Sakatare na Ma’aikatar Gwamnati, wakilin Majalisar Masarautar Kano, Wakilin Kudu, da kuma Darakta guda a matsayin masu tsaya wa wadanda ake tsare da su.

Dakta Kofar Mata ya ce sun gabatar da Daraktoci a matsayin masu tsaya wa mutanen, amma ya yi zargin cewa Alƙalin ya ƙi karɓar su, lamarin da ya sa suka nemi a yi adalci kan tsare mambobin nasu.

Kofar Mata ya yi gargadin cewa za su kuma shigar da irin wannan ƙara a gaban ƙungiyoyin ƙasa da ƙasa, ƙungiyoyin kare haƙƙin bil’adama, ’yan sanda da sauran hukumomin tsaro domin neman adalci da magance abin da suka bayyana a matsayin tsare mambobinsu ba bisa ƙa’ida ba.

Comments

Add a comment

Log in to the club or enter your details below.

A Biyo Mu a Shafukan Sada Zumunta

Today's Weather

  • Kano

    Thunder storm

    High: 32°C | Low: 22°C