On Air Now

ZANGON BARKA DA SAFIYA

5:00am - 10:00am

Kwankwaso Ya Gana Da Wike

Dan Takarar shugaban Kasa a karkashin jam’iyyar NNPP, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso Ya ziyarci gwamnan jihar Ribas Nyesom Wike a ranar Juma’a a birnin Fatakwal.

A yayin da babu masaniyar makasudin ganawar zuwa wannan lokaci, Sai dai kuma alamu na baiyana cewa  bata  rasa nasaba da Babban zabe  kasar nan shekarar   2023 dake tafe.

Kazalika shima tsohon gwamnan jihar Ekiti, Ayodele Fayose na a wajen yayin ganawar da mutanen biyu suka yi.

Ziyarar Kwankwaso na zuwa ne a yayin da shima Dan Takarar Shugaban kasa na jam’iyyar LP Peter Obi, da Gwamna Bala Mohammed na jihar Bauchi suka kai makamanciyar wannan ziyara a ranar Alhamis din data gabata ga gwamna Wike.