Ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa na jam'iyyar (NDC) a zaɓen 2027, Rabiu Musa Kwankwaso, ya yi kira da a farfaɗo da haɗin kan siyasa tsakanin Arewacin Najeriya da yankin Kudu maso Gabas.
Tsohon gwamnan Jihar Kano ya ce yankunan biyu na da dogon tarihin haɗin gwiwar siyasa wanda ya kamata a sake farfaɗo da shi.
Kwankwaso ya bayyana hakan ne a wata hira da ya yi da BBC Igbo, wadda aka wallafa a shafin Facebook na kafar yaɗa labaran a ranar Laraba.
Ya ce shugabannin siyasar Najeriya sun nuna muhimmancin sulhu da haɗa kan al'umma tsawon shekaru, musamman bayan yaƙin basasa, inda ya buƙaci 'yan Najeriya su rungumi yafiya da haɗin kan ƙasa.
Comments
Add a comment