On Air Now

ZANGON MARAICE

3:00pm - 8:00pm

Likitan Hakori Zai Duba Buhari

BUHARI

Fadar shugaban kasa ta ce shugaban kasa Muhammadu Buhari zai yi karin mako guda a birnin Landan, bisa bukatar da likitansa na Hakori ya nema,sakamakon duba shi da ya fara yi.

Mai magana da yawun shugaban kasar,  Femi Adesina, shi  ne ya tabbatar da haka  ta  cikin  wata sanarwa da ya fitar a Abuja a daren jiya.

Adesina ya ce kwararren likitan  na bukatar ganin shugaban kasar nan da wasu kwanaki biyar domin duba lafiyar  hakoransa.

Idan  ba’a manta  ba  Shugaba Buhari ya bi sahun sauran shugabannin duniya wajemn  halartar bikin nadin sarautar Sarki Charles  na ukku  a ranar 6 ga  watan  Mayun da muke  ciki.