On Air Now

ZANGON BARKA DA SAFIYA

5:00am - 10:00am

Likitoci 533 Ne Kadai Gwamnatin Jihar Kano Ke Dasu A Matsayin Ma'aikatanta.

LIKTOCI

kungiyar Likitoci ta kasa reshen jihar Kano ta koka kan yadda matsalar Likitoci dake tafiya kasashen waje aiki ke shafar bangaren kiwon lafiya a jihar kano, inda ta ce likitoci 533 ne kawai ke karbar albashin gwamnatin jihar Kano a yanzu haka.

Shugaban Kungiyar na  jihar  Kano, Dr. Abdullahi Kabir Sulaiman, shine ya bayyana haka a lokacin da yake zantawa da manema labarai a ranar Talata a nan birnin  Kano, inda ya dora alhakin matsalar kan  rashin kyawun aiki da albashin mai inganci ga  ma’aikatan lafiya.

Sulaiman ya ce likitoci da dama sun bar  aikin gwamnati  a matakin jihar kano inda suka koma  yin ayyuka a asibitocin gwamnatin tarayya da sauran jihohin da ke da ingantattun kayan aiki da kuma  albashi mai inganci.

A saboda haka ya shawarci gwamnatin jihar Kano  da ta magance matsalar banbancin albashin ma’aikatan lafiya da ake samu tsakanin  ma’aikatan  lafiya na  jiha da na tarayya domin magance matsalar ficewar  likitoci da ake samu zuwa kasashen waje domin yin aiki.