On Air Now

Off Air

Midnight - Noon

Likitoci Masu Neman Kwarewa Zasu Fara Yajin Aiki Ranar Laraba

Kungiyar Likitoci masu neman kwarewa ta baiyana cewar duk da sabon matsayar da gwamnatin taraiyya ta dauka, kan kudirin dokar wajabta yin aikin shekara biyar a kasar nan kafin Likita ya samu lasisin aiki, Hakan ba zai hana ta shiga yajin aikin gargadi na tsawon kwanaki biyar ba.

Shugaban kungiyar na kasa, Dr Innocent  Orji  ne ya baiyana haka lokacin da yake ganawa da manema Labarai , kan  abubuwan  da suka tattauna a  yayin taron kolin kungiyar  na kasa.

Ya  ce  zasu  fara yajin aikin ne  tun daga karfe  8 na safiyar  ranar  Laraba.  Wasu  alamu dai na nuni da cewar  ba iya  kudirin dokar  kadai bane,abunda  yake damun likitocin masu neman kwarewa.

A ranar  29  ga watan Aprilun bana ne  kungiyar  ta fitar da sanarwar jan kunne, tare da baiwa  gwamnatin taraiyya wa’adin  makwanni biyu,  data  aiwatar  da karin albashin likitoci  na bai  daya,  CONMESS  ko  kuma ta fuskanci  tafiya yajin aiki.