On Air Now

ZANGON RANA

10:00am - 3:00pm

Likitoci Masu Neman Kwarewa Zasu Fara Yajin Aikin Sai Baba Ta Gani

LIKITA

Kungiyar Likitoci masu neman Kwarewa ta kasa ta aiyana tafiya yajin aikin sai baba ta gani, sakamakon kin biyanta hakkokinta na alawus da kuma sauran wasu bukatu.

Shugaban kungiyar  na kasa, Dr. Orji Emeka Innocent,  shi ne  ya  bada  sanarwar  shiga  yajin aikin a daren jiya,  jim kadan bayan kammala  zaman kolin kungiyar  a Legas.

Ya ce  zasu  fara  yajin aikin ne da tsakar daren yau, Inda  ya baiyana bukatun da suke neman gwamnati ta biya masu, wanda  ya hada  da  biyansu  alawus  na daukar  horo.

Sauran bukatun sun hada  kudaden ariyas  da kuma sake  yin  nazari  kan tsarin biyansu  albashi   da dai sauransu.