On Air Now

ZANGON BARKA DA SAFIYA

5:00am - 10:00am

Likitoci Sun Nuna Rashin Amincewarsu Da Wajabta Yin Aikin Shekara Biyar A Najeriya

LIKITOCI

Kungiyar likitoci ta kasa masu zaman kansu ta kalubalanci yunkurin majalisar wakilai ta kasa na wajabta yin aikin tsawon shekara biyar a Najeriya ga duk wani Likita mai lasisi dake kasar nan.

Shugaban kungiyar na kasa,Dr Kayode Adesola  ne  ya baiyana haka yayin hirarsa da manema Labarai a birnin Ikko, Ya ce  yunkurin  aiwatar da kudin dokar  an yita ba bisa tsari  ba, wanda  zauren majalisar  ke tunanin yin haka  zai magane  matsalar ficewar  likitoci zuwa kasashen waje.

Ya kara  da cewar  yadda  aka gabatar da kudurin dokar,Ya nuna cewar  ba’a yi wani kyakykyawan nazari da bincike ko kuma tattaunawa da masu ruwa  da tsaki a fannin domin jin  ta bakinsu  kan illolin dake  tattare da yin hakan.

Ya kuma kara da cewar  Likitocin kasar  basa  bukatar  samun wani Lasisi  daga Najeriya domin samun damar yin aiki a wasu kasashe,A saboda  haka sai ya yi kira  da ‘a saka dokar  ta  baci a bangaren kiwon lafiya  na kasar  nan, domin magance  tarin kalubalen dake   damun bangaren.