On Air Now

Off Air

Midnight - 5:00am

Litar Mai Zata Koma Naira 360 zuwa 400 Idan Aka Cire Tallafin Mai

PENGASSAN

Kungiyar manyan ma’aikatan mai da kuma iskar gas ta kasa PENGASSAN,Ta ce za’a rika siyar da litar man fetir tsakanin naira 360 zuwa 400 bayan janye tallafin man fetir da gwamnati ke biya.

Shugaban kungiyar na kasa,Festus  Osifo ne ya baiyana haka ga manema Labarai a jiya, a gefen taron kolin kungiyar da aka shirya a Abuja  babban birnin taraiyya.

Sai dai kuma ya  ce  kungiyar ta umarci daukacin mambobinta dake  fadin kasa  dasu tabbatar sun  samar  da wadataccen mai  ga  yan Najeriya,tare da yin barazanar kwace  lasisin duk wani dan kungiyar da aka samu yana boye man fetir.