On Air Now

ZANGON BARKA DA SAFIYA

5:00am - 10:00am

Litar Man Fetir Ta Haura Dubu 1 A Jihar Ebonyi

MAN FETIR

Farashin man fetur ya karu zuwa Naira Dubu 1 da 200 kan kowace lita a Abakaliki, babban birnin jihar Ebonyi a jiya, Tun bayan da shugaban kasa Bola Tinubu ya aiyana cire tallafin mai.

Wani mazaunin birnin mai suna, Darlington Okeke, ya danganta matsalar  da  yawan  siyan man da jama’a  ke yi,  sakamakon shiga  yanayin razana kan yuyuwar samun karancin man, tun bayan  furucin da  Tinubun ya yi a ranar  Litinin.

Hakazalika farashin man fetur ya yi tashin gwauron zabo zuwa Naira 600 a kan  kowace lita a mafi  akasarin  sassan kasar nan, lamarin da ya sa aka samu tashin kudin sufuri  da kimanin kaso 100 bisa 100.

Dogayen layukan dai sun sake kunno kai a gidajen mai a  jihohin  Legas  da  Abuja  sai  Ilorin da  Benin  da  birnin   Asaba  da birnin  Fatakwal  sai nan jihar  Kano  da  birnin  Makurdi da sauran manyan biranen dake  kasar  nan.