On Air Now

ZANGON RANA

10:00am - 3:00pm

Litar Man Fetir Zata Haura Naira 700 A JIhar Kano

FETIR

Dillalan Man fetir sunyi hasashen cewar farashin litar man fetir zata iya haura naira 700 a nan jihar Kano da wasu jihohin Arewacin kasar nan, daga wata mai kamawa na Yuli.

Shugaban kungiyar  dilallan man fetir  ta kasa  masu zaman kansu, IPMAN, Mike Osatuyi, Ya  fadawa manema Labarai  cewar, Farashin litar  man  fetir  zata iya haura naira 700 a  yankin arewacin kasar  nan,  da  zarar  ‘yan kasuwar  mai sun  fara  dauko  sabon man fetir  a   wata mai kamawa.

Ya kara da cewar  mutanen dake zaune a yankin Arewacin kasar  nan zasu  rika  biyan  sama da naira  700  kan kowace litar  man  fetir,  Yayin da wadanda suke a wajen jihar Legas, zasu  rika sayen litar man  fetir din sama da naira  610,  sai kuma wadanda  suke  zaune a cikin birnin Ikko,  da zasu rika  sayen litar  man fetir  din kan naira  600.