On Air Now

ZANGON SAFIYAR LAHADI

5:00am - Noon

Ma'aikata Sun Koka Kan Tsadar Rayuwa Da Gwamnatin Buhari Ta Jefa Su Ciki

MA'AIKATA

A yayin da shugaban kasa Muhammadu Buhari zai gudanar da bukin ranar ma’aikata ta karshe a matsayinsa na shugaban kasa a yau, kungiyoyin kwadago sun baiyana kwazon gwamnati mai ci tare da gwamnatocin jihohi a matsayin wanda ba yabo ba fallasa,Suna masu baiyana cewar ‘yan Najeriya sunsha fama da matsala ta tsadar rayuwa.

Da yake magana dangane da ranar  Ma’aikata,  Ma’ajin kungiyar kwadago  ta NLC Hakeem Ambali, Ya  ce  gwamnati  mai ci  ta jefa  ma’aikatan  kasar  nan  cikin  kunchin rayuwa da wahalhalu  iri-iri.

Ya kara da cewar  wasu ma’aikatan sun rasa  aikinsu  a  yayin da matsalar  rashin tsaro da  tsadar rayuwa  da sauran wasu matsaloli a  karkashin gwamnatin Buhari  suka jefa  jama’a  da dama  cikin kangin rayuwa.

To sai dai kuma a martanin da fadar  shugaban  kasa  ta  yi,  Ta jaddada cewar  shugaban kasa Muhammadu Buhari ya taka rawar azo a gani  kan samun cigaban kasar  nan, duk kuwa  tarin sukar  da  yake  fuskanta,  Tana  mai  cewar  zai sauka  mulkin kasar nan  ne  ba  kamar  lokacin da  same  ta tana cikin wanayi  na ban tausayi ba.

Wata sanarwa  da tawagar  masu  kula da harkokin sadarwa  na fadar  shugaban kasa  suka  fitar  mai dauke da shafuka 91  a ranar  Lahadi,  Sun baiyana irin dimbin nasarorin da gwamnatin shugaban kasa muhammadu Buhari ta samu a cikin shekara Takwas  da  yayi  yana  mulkin kasar  nan,  inda suka yi  bayani kan wasu bangarori  har  guda  20.

Sanarwar  mai dauke dasa hannun kakakin shugaban kasa, Femi Adesina , Ta  baiyana cewar  shugaban kasar  ya zama  tamkar  wanda  ya tsamo kitse  daga  wuta  kan  halin da  ya samu kasar  nan.