On Air Now

Off Air

Noon - 6:00pm

Ma'aikatan Jihar Benue Sun Koka Kan Tulin Bashi Albashi Da Fansho Da Suke Bin Gwamnati

Samuel Ortom

Shugaban kungiyar kwadago ta kasa reshen jihar Benue, Terungwa Igbe, ya bukaci gwamnatin jihar da ta temaka ta biya dukkanin wasu basussukan albashin ma’aikata da kuma na fansho da ake binta.

Igbe, wanda ya koka kan halin da ma’aikata ke ciki a jihar, ya yi wannan kiran ne a sakatariyar jihar da ke kan titin Otukpo maimakon dandalin   taro na  IBB, wurin da ma’aikata suka saba gudanar da bikin ranar  ma’aikata  a kowace  shekara.

Ya ce ma’aikatan sun zabi gudanar da bukukuwan   ne  batare  da yin gagarumin wasu taruka ba, saboda  basussukan albashi da ake bin  gwamnatin jihar.

Shugaban  kungiyar  ta  NLC ya kuma bukaci a  mayar da shekarun ritayar ma’aikata daga shekara 35 zuwa shekara 40, da kuma cika shekaru 65  a  matsayin na  ritaya a maimakon shekaru 60 da ake yi a yanzu.