On Air Now

ZANGON RANA

10:00am - 3:00pm

Ma'aikata A Jihar Kano Na Cikin Barazanar Shiga Wani Yanayi - Shugaban NLC Comrade Minjibir

Kungiyar kwadago ta kasa NLC reshen jiahr Kano ta bayyana matukar damuwarta akan yadda matsalolin biyan kudin fansho da gratuity a  jihar Kano ke neman Jefa ma’aikata a jihar Kano cikin Mummunan yanayi.

Shugaban kungiyar ta NLC a Kano Comrade Kabiru Ado Minjibir shine ya yi wannan koke yayin wata liyafar karrama sabon zababben shugaban kungiyar ma’aikatan rediyo da talabijin, reshen Kano RATTAWU, Babangida Mumuda.

Minjibir yace tun a shekarar 2006, lokacin Gwamna Malam Ibrahim Shekarau, tsarin Pansho ya fara samun matsala yadda ake gaza turawa hukumar Pansho kaso 17 cikin 100 na Albashin ma’aikata da doka ta tanada a matakin kananan hukumomi da hokumar SUBEB da matakin ma’aikatan kula da lafiya matakin farko, wanda matsalar ke cigaba da girmama har zuwa wannan gwamnati, kuma sun gabatar da kokensu ga gwamnan jihar Kano Dr Abdullahi Umar Ganduje, inda ya umarci hukumomin da abin ya shafa da su rika biyan kudaden  amma sun bijirewa umarnin.

Minjibir yace kawo yanzu kudaden Gratuty ya kai Naira biliyan arba'in da ba’a biya ma’aikata da suka kammala yiwa Kano hidima ba, yana mai kira ga gwamna Dr Abdullahi Umar Ganduje duba matsalar.

Kano NLC

Da yake zantawa da wakilinmu Bashir Faruk Durumin Iya, sabon zababben shugaban kungiyar ma’aikatan rediyo da talabijin RATTAWU reshen Kano, Babangida Mamuda Biyamusu, ya yi alkawarin bayar da hadin kai tare da yin aiki kafada da kafada da shuwagabanni da mambobin kungiyar domin bunkasa fannin.