On Air Now

ZANGON DARE

8:00pm - Midnight

Ma'aikatan Kwashe Shara A Abuja Sunyi Barazanar Rufe Makabartun Abuja Idan Ba'a Biya Masu Bukatunsu Ba

MAKABARTA

Ma’aikatan kwashe shara dake karkashin Hukumar kula da Muhalli ta birnin taraiyya Abuja, Sunyi barazanar rufe daukacin makabartu dake birnin taraiyya Abuja.

A ranar Laraba ne, Ma’aikatan suka rufe  Makabartar Gudu dake Abuja, amma hukumar birnin taraiyya Abuja tayi gaggawar daukar mataki akan matsalar.

Da yake jawabi ga manema Labarai,  Shugaban gamaiyyar kungiyar kungiyoyin Ma’aikatan gwamnatin na Abuja, Kwamared Muktar Bala, Yace kungiyar ba zata yi kasa a gwiwa ba wajen rufe daukacin makabartun dake Abuja muddin ba’a biya masu bukatunsu ba.

A yanzu haka ma’aikatan kwashe sharar na  yajin aiki sakamakon abunda suka baiyana  na rashin aiwatar masu da sabon  tsarin  albashi da aka amince masu dashi tun a shekarar  2019.