On Air Now

Off Air

Noon - 6:00pm

Ma'aikatan Sufurin Jiragen Sama Sun Janye Aniyarsu Ta Shiga Yajin Aikin Sai Baba Ta Gani

Kungiyoyin ma’aikatan sufurin jiragen sama sun dakatar da shirinsu na tafiya yajin aikin sai baba ta gani, sakamakon ganawar da suka yi tsakaninsu da jami’an ma’aikatar sufurin jiragen sama ta kasa.

Kungiyoyin sun baiyana  matakin nasu ne  ta cikin wata wata sanarwa da aka fitar a  birnin taraiyya Abuja.

Sanarwar  ta baiyana cewar  kungiyoyin sunyi la’akari ne da abunda zai zama  masalaha  ga  bangaren  sufurin jiragen sama a kasar  nan, A yayin da zasu yi dakon  matakin da gwamnatin taraiyya zata dauka  a  yayin ganawar da zasu yi ranar  9 ga watan nan na Mayu.

Janye shirin tafiya yajin aikin na zuwa ne , kasa da mako daya bayan da kungiyoyin sufurin jiragen sama suka yi barazanar tsunduma yajin aikin sai baba ta gani, sakamakon matsalolin da suka danganci biyansu albashi da  rashin kyawun yanayin gudanar da aiyuka a  tsakanin  ‘ya’yansu.