Wani mutum mai shekaru 40 da 'yarsa mai shekaru 13 sun rasu bayan sun shiga wata busasshiyar rijiya domin ɗauko wayar hannu a ƙauyen Taka-tsaba da ke ƙaramar hukumar Tsanyawa ta Jihar Kano.
Rahotanni sun bayyana cewa marigayin, Abubakar Na Baba, ya saukar da 'yarsa Fiddausi cikin rijiyar ta hanyar amfani da igiya, kafin shi ma ya shiga domin cetonta bayan ta daina ba da amsa.
Wani mazaunin ƙauyen, Malam Sa'adu Gambo, ya ce lokacin da jami'an agajin gaggawa suka isa wurin, an yi imanin cewa mahaifin da 'yarsa sun riga sun rasu.
Ya ƙara da cewa tsananin zafin da ke cikin rijiyar ya sa aikin ciro gawarwakin ya kasance mai matuƙar wahala ga jami'an kashe gobara.
Comments
Add a comment