On Air Now

ZANGON MARAICE

3:00pm - 8:00pm

Mahaifiyar Tsohon Shugaban Majalissar Wakilan Najeriya Ta Rasu A Jihar Kano

Allah ya yiwa mahaifiyar Rt Hon Ghali Umar Na’abba, tsohon kakakin majalisar wakilai, Hajiya Rabi Rasuwa.

Rahotanni sun bayyana cewa, Hajiya Rabi ta rasu ne a Kano a daren jiya bayan ta yi fama da gajeriyar rashin lafiya kamar yadda wata majiya daga iyalan gidan ta tabbatar wa manema labarai.

Bayanan da aka samu sunce za’ayi Jana’izar Hajiya Rabi  da safiyar yau juma’a da karfe 10 na safe a gidan marigayi  Bashir Tofa dake unguwar Gandun Albasa a Kano.

More from Labarai