On Air Now

ZANGON RANA

10:00am - 3:00pm

Mai Horas Da Super Eagles Ya Isa Uyo Gabanin Wasan Da Kungiyar Zata Yi Da Sao Tome and Principe

Mai horas da tawagar Super Eagles tan an gida Najeriya Jose Peseiro ya isa birnin Uyo gabanin wasan neman tikitin shiga gasar cin kofin Afrika da za su kara da Sao Tome and Principe.

Peseiro wanda kwanakin baya ya amince da tsawaita kwantiraginsa ya isa birnin Uyo tare da mataimakansa a ranar Talata.

Najeriya za ta kara da Sao Tome and Principe ranar Lahadi a filin wasa na Godswill Akpabio dake  Uyo.

Hukumar kwallon kafa  ta nahiyar Afrika  ta nada alkalin wasa Lahlou Benbraham dan kasar Algeria a matsayin wanda zai busa  wasan.