On Air Now

ZANGON BARKA DA SAFIYA

5:00am - 10:00am

Mai Juna Biyu Ta Gamu Da Ajalinta Saboda Yajin Aikin Likitoci A Jihar Nasarawa

Wata mata mai matsakaicin shekaru a jiya rahotanni sun bayyana cewa ta rasa ranta a jihar Nasarawa saboda rashin likita da zai duba ta.

Hakan ya biyo bayan yajin aikin gargadi na kwanaki biyar da likitoci masu neman kwarewa reshen asibitin kwararru na  Dalhatu da ke Lafiya suka gudanar.

Matar mai juna biyu wadda ba a bayyana sunanta ba a asibitin kwararru na Dalhatu da ke Lafiya, rahotanni sunce an tsara za’ayi ma ta tiyata.

Sai dai aikin bai samu ba saboda yajin aikin gargadi na kwanaki biyar.

Ta rasu ne a lokacin da take jiran likitoci su kula da ita.