On Air Now

ZANGON RANA

10:00am - 3:00pm

Mai Martaba Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero, Ya Jagoranci Jana'izar Limamin Waje

Mai Martaba Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero, ya jagoranci Jana'zar marigayi limamin waje Wazirin Kano murabus Sheikh Nasir Muhammad Nasir.

An dai gudanar da Sallar Jana'zar ne da Karfe 9 na safiyar ranar Alhamis a Kofar Kudu fadar Mai Martaba Sarkin Kano.

Mai Martaba Sarkin Bichi Alhaji Nasiru Ado Bayero yana daga cikin manyan mutane da suka halarci Jana'zar, da sauran manyan Mutane da Shehunnai da limamai da Yan Kasuwa da sauran al'uma.

Wata sanarwa da babban Sakataren yada labarai na Masarautar Kano, Abubakar Balarabe Kofar Naisa, ya fitar ta rawaito cewa bayan idar da Sallar Jana'zar ne Mai Martaba Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero da dan uwansa mai Martaba Sarkin Bichi Alhaji Nasiru Ado Bayero da sauran daruruwan al'umma aka tafi rakiyar gawar Marigayin.

An dai binne marigayi Sheikh Nisir Muhammad Nasir ne a Makabartar Dan Dolo dake Gordon Dutse cikin yankin Karamar Hukumar Gwale dake Birnin Kano.

Mai Martaba Sarkin yayi addu'ar Allah ya gafarta masa yasa aljanna makoma a gareshi tareda baiwa iyalai da "Yan uwa da sauran al'uma hakurin jure rashin Wazirin Kano Murabus kuma Limamin Waje Sheikh Nisir Muhammad Nasir.

Kafin rasuwarsa Sheikh Nisir Muhammad Nasir babban Amini ne ga marigayi Sarkin Kano Alhaji Dr. Ado Bayero Wanda ya bayar da gudunmawa a bangarori daban daban ta hanyar cusa kyawawan dabi'u ga matasa da cusa musu soyayyar Annabi Muhammadu (S.A.W.)

Sheikh Nisir Muhammad Nasir ya rasu yabar matansa na aure da Yaya da kuma jikoki masu yawa.