On Air Now

Off Air

Midnight - 5:00am

Mai Martaba Sarkin Kano Ya Dawo Birnin Dabo Bayan Kammala Umrah

Bayan kwashe kwanaki 8 yana gudanar da zirayar aikin Umrah Mai Martaba Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero ya dawo Gida Kano.

Alhaji Aminu Ado Bayero ya sauka a filin sauka a filin sauka da tashi na kasa da ksa na Aminu dake nan Kano tareda dan uwansa Sarkin Bichi Alhaji Nasiru Ado Bayero da Sarkin Bauchi Alhaji Dr. Rilwanu Sulaiman Adamu.

A lokacin ziyarar aikin Umrah a kasa mai tsarki Mai Martaba Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero yana tareda Shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Ta cikin wata sanarwa da ya aikowa Arewa Radio, sakataren yada labarai na masarautar Kano, Abubakar Balarabe Kofar Naisa, ya rawaito, a lokacin saukar Mai Martaba Sarkin Kano ya sami tarba daga Hakimansa da sauran manyan yan Kasuwa tareda al'umar gari wadanda sukayi dafifi akan titi suna lale marhabun da zuwan uban kasa.