Sanatan da ke wakiltar Kaduna ta Kudu a Majalisar Dattawa, Sunday Katung, ya bukaci al'umma su kwantar da hankalinsu tare da mutunta bukatar iyalan marigayiya Mary Habila bayan rasuwarta a gidan ministan aiyuka na tarayya, Dave Umahi.
A cikin wata sanarwa da mai ba shi shawara kan harkokin yada labarai, Midat Joseph, ya fitar a ranar Asabar, Sanatan ya roki jama'a da su guji duk wani abu ko kalaman da ka iya tayar da hankali ko kawo cikas ga zaman lafiya.
Ya ce duk da cewa al'umma na cikin jimami da alhini sakamakon lamarin, bai kamata hakan ya jawo aikata abin da zai iya jefa rayuka cikin hadari, kawo cikas ga doka da oda, ko kuma shafar gudanar da bincike yadda ya kamata ba.
Katung ya kuma bukaci jama'a su mutunta bukatar iyalan marigayiyar na yin makoki cikin sirri tare da binne diyarsu cikin mutunci ba tare da an farka ta ba domin gano musabbabin mutuwar ta ta.
Ya ce iyalan sun bayyana cewa ba sa son katsalandan ko zarge-zargen da za su biyo bayan wannan lamari. Ya kara da cewa wannan roko ya shafi takwarorinsa a Majalisar Dokoki ta Kasa da kuma dimbin masu yi musu jaje daga cikin da wajen Najeriya da suka tuntube shi domin neman karin bayani.
Sanatan ya bayyana rasuwar Mary a matsayin babban rashi mai sosa zuciya wanda ya jefa iyalanta, abokanta da al'ummar Kaduna ta Kudu cikin jimami. Ya kuma mika ta'aziyyarsa ga iyalan marigayiyar tare da addu'ar Allah Ya jikanta, Ya kuma ba iyalanta hakurin jure wannan babban rashi.
Ya bayyana fatansa cewa hukumomin da abin ya shafa za su gudanar da cikakken bincike cikin adalci da gaskiya kan yadda lamarin ya faru, bisa tanadin doka, domin gano gaskiya da tabbatar da adalci. Ya ce a duk tsawon wannan tsari ya kamata a mutunta ra'ayi da bukatun iyalan marigayiyar.
Har ila yau, Sanatan ya ce ya tabbatar wa iyayen Mary cewa ofishinsa zai ci gaba da tabbatar da an yi musu adalci tare da daukar dukkan matakan da doka ta tanada domin taimaka musu samun amsoshin da suke nema.
Marigayiya Mary Habila na cikin tawagar ma'aikatan lafiya da suka raka Ministan Ayyuka, David Umahi, zuwa garinsu na Uburu da ke karamar hukumar Ohaozara, inda aka ce an tsinci gawarta a cikin harabar gidan Ministan.
Comments
Add a comment