On Air Now

ZANGON RANA

10:00am - 3:00pm

Majalisar Dattawa Zata Baiyana Sunayen Ministoci

GODSWIL AKPABIO

Kowane lokaci daga yanzu, Ana saran Shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio, zai bayyana sunayen wadanda ake son nadawa kan matsayin ministoci a zauren majalisar dattawa a cikin wannan mako da muka shiga.

Yanzu haka dai ana cigaba da tofa albarkacin baki  kan  jinkirin da shugaba Bola Tinubu ya yi wajen kafa majalisar ministocinsa kimanin watanni biyu bayan rantsar da shi a matsayin sabon shugaban kasa.

Kazalika kundin tsarin mulkin kasa  ya  umurci shugaban  kasa  da   gwamnoni su kaddamar da majalisar zartarwarsu a  cikin kwanaki 60 na farko a kan karagar mulki.

Sai dai wasu majiyoyi daga majalisar sun shaidawa jaridar Punch cewa wasikar da ke kunshe da sunayen wadanda ake son nadawa  kan matsayin ministoci  ta isa  wajen  shugaban majalisar dattawa a makon jiya.

Majiyar ta kara da cewa an yi wasu gyare-gyare a cikin jerin sunayen   mutananen, wanda hakan ya sa aka jinkirta karanta sunayen.