On Air Now

ZANGON RANA

10:00am - 3:00pm

Majalisar Dinkin Duniya Ta Tabbatar Da Sa Ce Yan Mata Sama Da 200 Dake Gudun Hijira A Jihar Borno

Majalisar Dinkin Duniya

Majalisar dinkin duniya ta tabbatar da yin garkuwa da wasu ‘yan mata sama da 200 dake yin gudun hijira a jihar Borno.

Jami’in tuntuba kan harkokin bada tallafi  na majalisar a nan Najeriya, Mohammed Malick Fall ne ya baiyana haka ta cikin wata sanarwa da aka fitar a daren jiya, Inda  ya ce  suna cikin jimamin abunda  ya  faru.

Sanarwar  ta baiyana cewar ba’a san adadin ‘yan matan da aka sace ba zuwa wannan lokaci, amma  dai tana kiyasin sun zarta  200.

Sa’oi  48 tun bayan garkuwa da  tarin ‘yan matan da aka yi, zuwa yanzu hukumomin tsaro da kuma shugabannin siyasa a kasar nan, sunki  bada  tabbacin abun ya faru ko kuma akasin haka.

Wasu dangin  ‘yan matan da aka sace  sun fadawa jaridar Daily trust cewar , suna  jin cewar  an  wofantar  dasu, biyo bayan shurun da hukumomi  suka yi, tare da yin kira ga  a gare su  da  su yi abunda  ya da  ce domin kubutar masu da ‘yan uwan nasu, don kaucewa maimaita irin abunda  ya  faru  kan ‘yan matan Chibok  da aka sace a shekarar  2014.