On Air Now

ZANGON MARAICE

3:00pm - 8:00pm

Majalisar Dokokin Jihar Legas Ta Amince Da Sama Da Naira Tiriliyan 1 A Matsayin Kasafin Kudin 2023

Gwamna Babajide Sanwo Olu

Majalisar dokokin jihar Legas ta amince da naira tiriliyan 1 da bilyan 768 a matsayin kasafin kudin jihar na shekarar 2023.

kasafin kudin da aka amince da shi ya nuna cewar  za’a kashe Naira bilyan 748 a bangaren aiyukan yau da kullum sai kuma sama da Naira tiriliyan 1 da za’a yi amfani da ita  a bangaren gudanar da manyan  ayyuka.

A watan Oktoban bana ne, Gwamna Babajide sanwo-olu ya gabatar da kasafin kudin jihar wanda ya kama  naira tiriliyan 1 da bilyan  69  ga majalisar dokokin jihar.