On Air Now

ZANGON RANA

10:00am - 3:00pm

Majalisar Dokokin Jihar Ondo Na Shirin Aiyana Mataimakin Gwamnan Jihar A Matsayin Mukaddashin Gwamna

Bayan wata ganawar sulhu da shugaban Kasa Bola Tinubu ya yi da jagororin jihar Ondo a ranar Juma’ar data gabata, A halin yanzu ‘yan Majalisar dokokin jihar zasu gana a yau domin tattauna yanayin siyasar da jihar ke ciki.

Wata majiya daga  zauren majalisar  dokokin  jihar  ta fadawa  jaridar  Punch cewar, Daya daga cikin manyan abubuwan da ‘yan majalisar  zasu tattauna  shi ne,  Yiyuwar aiyana mataimakin gwamnan jihar Lucky Aiyedatiwa  a matsayin mukaddashin gwamnan jihar, biyo bayan dogon lokacin da aka dauka batare da ganin fuskar gwamnan  a jihar ba.

A lokacin da aka tuntubi kakakin majalisar  Olamide Oladije domin jin ta bakinsa, Ya  ce  yana  cikin taro ne, kuma kawo yanzu da  muke baku labarin babu wata amsa da  ya  bayar.

Majalisar dai ta jingine kudirinta na  tsige mataimakin gwamnan jihar  daga kan kujerarsa  tun bayan  ganawar da suka yi da shugaban Kasa Bola Tinubu.