Majalisar Dokokin Jihar Kano ta bayyana damuwarta kan yadda wasu dillalan gidaje ke karɓar kuɗaɗe masu yawa ba bisa ƙa'ida ba daga masu neman hayar gida a faɗin jihar.
Kakakin Majalisar, Rt. Hon. Jibril Ismail Falgore ne ya bayyana hakan yayin da yake mayar da martani kan rahotannin da ke zargin wasu dillalan gidaje da cin zarafin masu neman masauki ta hanyar karɓar kuɗaɗe masu tsanani.
Ya ce irin wannan ɗabi'a na ƙara wa al'umma nauyi, musamman masu neman gidajen haya.
Da yake magana da wakilinmu, Arewa Radio, ta bakin Babban Sakataren Yaɗa Labaransa, Kamaludeen Sani Shawai, Falgore ya bayyana kuɗaɗen da ake karɓa a matsayin masu yawa fiye da kima, yana mai cewa hakan na haifar da zargin danniya da rashin adalci.
Ya ce Majalisar ba ta gamsu da wannan lamari ba, tare da kira ga hukumomin da abin ya shafa da sauran masu ruwa da tsaki da su ɗauki matakin gaggawa domin kawo ƙarshen wannan matsala.
A bara, Gwamnatin Jihar Legas ta gabatar da wani sabon kudirin doka kan haya domin dakile karin kuɗin haya ba bisa ƙa'ida ba, da haramtattun kuɗaɗen da ake karɓa, tare da sauran hanyoyin da ake zargin ana cin zarafin masu haya a fannin gidaje.
Da take magana kan batun, kungiyar Masu Dillancin Gidaje ta Jihar Kano (KAFADA) ta danganta cigaba da hauhawar kuɗin hayar gidaje a faɗin jihar da rashin wata hukuma ta gwamnati da za ta tsara tare da sa ido kan harkar gidaje.
Mataimakin Shugaban ƙungiyar, Abdulhadi Iyan Hadi, ya ce kafa irin wannan hukuma zai ba masu haya damar ƙalubalantar karin kuɗin haya da ake yi ba bisa ƙa'ida ba, tare da ƙara tabbatar da gaskiya da riƙon amana a tsakanin masu gidaje da dillalan gidaje.

Ya shaida wa Arewa Radio cewa KAFADA ta rubuta wa Gwamnatin Jihar Kano har sau tara tare da gabatar da shawarwari kan yadda za a magance matsalar, amma har yanzu ba a gayyaci ƙungiyar domin tattaunawa a hukumance kan batun ba.
Iyan Hadi ya kuma ɗora alhakin hauhawar kuɗin hayar gidaje kan ayyukan dillalan gidaje da ba su da rajista, yana mai gargadin cewa matsalar za ta cigaba muddin gwamnati ba ta kafa tsarin doka da hukuma da za su tsara harkar dillancin gidaje a jihar ba.
Comments
Add a comment