On Air Now

Off Air

Midnight - Noon

Majalisar Tsaro Ta Jihar Kano Ta Ayyana Kwacen Waya Amtsayin Laifin Fashi Da Makami

Majalisar tsaro ta jihar Kano ta ayyana satar waya a matsayin fashi da makami, kuma duk wani mutum ko kungiya da aka kama da aikata laifin za su fuskanci hukuncin  hakan.

Kwamishinan yada labarai da harkokin cikin gida mai barin gado, Malam Muhammad Garba ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya raba wa manema labarai a Kano.

Majalisar da Gwamna mai barin gado Abdullahi Umar Ganduje ya jagoranta a yayin zamanta na bankwana, ta bayyana cewa kwacen waya a ‘yan kwanakin nan ya kai wani matsayi abun damuwa don haka yana bukatar daukar tsauraran matakai.

Sanarwar ta kuma bayyana cewa majalisar ta amince da samar da wata tawaga ta musamman a cikin tsarin tsaro domin tunkarar matsalolin da ke faruwa a jihar.

“Kwamishanan ya kara da cewa majalisar a yayin da take tattaunawa kan rantsar da sabon gwamna ta ce an dauki dukkan matakan da suka dace don ganin an gudanar da bukukuwan lami lafiya tare da gargadin cewa miyagu da za su yi amfani da wannan dama wajen haddasa tashin hankali da sunan biki da su guji yin hakan.

Ya godewa jami’an tsaro a jihar Kano bisa dukkan hadin kan da suka ba shi a tsawon mulkin sa.

Taron ya samu halartar kusan dukkan shugabannin hukumomin tsaro da sauran mambobin majalisar.