On Air Now

ZANGON DARE

8:00pm - Midnight

Majalisar Wakilai Ta Ce Ba Zata Zama 'Yar Amshin Shata Ba

Sabon kakakin zauren majalisar wakilai ta kasa, Tajudden Abbas ya yi alkawarin cewar zauren majalisar na goma ba zai kasance ‘Dan amshin shata ba.

Ya baiyana  haka ne  ga  wakilan kafafen yada labarai na fadar shugaban kasa dake Abuja, Jim kadan bayan ganawarsa da shugaban kasa, Bola Tinubu, bayan  yasha  rantsuwar kama aiki a jiya.

Ya  ce  ‘yan majalisar  wakilan sun zabi ra’ayinsu a faiyace sabanin  rahotannin da  wasu kafafen yada  labarai  suka   fitarwa.

Ya  kuma yi alkawarin cewar  bangaren majalisar  zai hada  kai  da  bangaren zartarwa domin samar da cigaban  da kasar  nan ke muradi,  tare  kuma  da  kalubalantar  tsare-tsaren  da  suka  ci karo  da  cigaban kasa.

Shima  a nasa jawabin, Shugaban majalisar dattawa  Sanata Godswill Akpabio,  Ya  ce  zauren majalisar  zai bada cikakken goyon bayansa  kan  cire  tallafin mai da shugaban kasa  Tinubu ya yi.