On Air Now

ZANGON RANA

10:00am - 3:00pm

Majalisar Wakilai Ta Goyi Bayan Shawarar Kara Haraji Akan Lemukan Sha

LEMUKAN SHA

Shugaban Kwamitin Kula da Lafiya na Majalisar Wakilai, Hon. Yusuf Tanko Sununu, ya goyi bayan shawarwarin da wata kungiya mai fafutikar ganin an samu raguwar cutar Siga a kasar nan ta bayar, na kara harajin da ake biya kan lemukan sha na zaki, zuwa naira 20 akan kowace lita daya a maimakon naira 10 da ake karba kan kowace lita.

Dokar Kudi ta 2021 ta amince das aka  harajin Naira 10 akan kowace lita daya ta  abubuwan sha masu zaki, da wadanda ba na barasa ba.

Sai dai kungiyar ta baiyana cewa kamata yi a  kara  da ake karba  ta bangaren domin magance kalubalen kiwon lafiya da ake fuskanta ta hanyar amfani da abubuwa masu zaki  da kuma ba da damar saka hannun jari a  bangaren samar da kayayyakin kiwon lafiya a kasar nan.

Da yake jawabi a lokacin da kungiyar ta kai masa ziyara ,  Dan Majalisar  ya baiyana cikakken goyon bayansa  kan shawarar  da suka bayar.