On Air Now

ZANGON MARAICEN LAHADI

6:00pm - Midnight

Majalisar Wakilai Ta Hana Gwamnatin Taraiyya Cefanar Da Kanfanin Sarrafa Karafa Na Ajaokuta

Ajakouta

A ranar Litinin ne, Majalisar wakilai ta bukaci gwamnatin tarayya da ta dakatar da shirin ta na cefanar da kamfanin sarrafa karafa na Ajaokuta da kamfanin hakar ma’adinai na kasa domin tuntubar masu ruwa da tsaki.

Majalisar ta amince da kudirin da Abdullahi Ibrahim Halims ya gabatar inda ta gayyaci ministan ma’adinai da karafa domin ya yi mata cikakken bayani kan shirin cefanar da kanfanonin biyu.

Dan majalisar  ya baiyana  shirin cefanar  da kanfanonin da tsakar rana, yayin da ya ragewa gwamnati mai ci kasa da  kwanaki 30 wa’adinta ya kare, bai dace  ba  kuma rashin kishin kasa ne.

Ya yi kira da a samar da wasu tsauraran sharudda  koda  za’a aiwatar da tsarin ba wai yinshi  sake babu kaidi ba.

Daga karshe majalisar  wakilan ta umarci kwamitinta mai kula da bangaren ma’adinai  da  ya  yi gaggawar  bincike kan lamarin.