On Air Now

ZANGON BARKA DA SAFIYA

5:00am - 10:00am

Majalisar Wakilai Zata Haramtawa Ma'aikatan Babban Bankin Kasa Shiga Harkokin Siyasa

Babban Bankin Kasa CBN

Majalisar wakilai ta fara wani yunkuri na hana ‘yan siyasa da masu ra’ayin siyasar samun mukamai a babban bankin kasa.

Kudirin dokar  Babban Bankin kasa  ta shekarar  2022  da ake yiwa gyaran fuska  wadda  ta tsallake karatu na biyu a zauren majalisar a ranar Talata, ta kuma yi tanadin hana masu rike  da mukamai a  babban bankin kasar shiga cikin harkokin siyasa.

Bugu da kari dokar  bankin ta shekarar  2007 tayi  tanadin  sake  saka wasu  sharudda  da ake bukatar mutum ya cika kafin samun matsayin gwamnan babban bankin ko mataimakinsa ko wani darekta a bankin da sauran wasu mukamai.

Dan Majalisar  Sada Soli  na jam’iyyar  APC daga jihar   Katsina wanda ya gabatar da kudirin,  ya ce gyaran  dokar bankin kasar ba anyi ta bane  bisa  son zuciya,  sai dai kawai domin inganta aiyukan bankin, wanda ya bada misali da yadda gwamnan bankin na yanzu  Godwin Emefiele ya garzaya kotu inda yake neman a bashi damar tsayawa takara.