On Air Now

ZANGON MARAICE

3:00pm - 8:00pm

Majalissar Dattawa Zata Tantance Sabbin Ministociin Buhari 7

'Yan Majalisar Dattawa za su tantance mutane bakwai da Shugaba Buhari ya miƙa sunayensu a makon da ya gabata domin nada su amatsayin Ministocinsa.

Shugaban Majalisar Dattawan Ahmad Lawan shine ya sanar da tantancewar a jiya Talata inda ya ce za a shafe zaman majalisar da za a yi yau domin tantance ministocin.

Cikin waɗanda za a tantance akwai Ibrahim El-Yakub daga Jihar Kano, Umana Okon Umana (Akwa Ibom), Henry Ikechukwu Iko (Abia), Ademola Adegoroye (Ondo), Odum Odi (Rivers).

Sauran su ne Goodluck Nnana Opia (Imo) da kuma Joseph Ukama (Ebonyi ).

Wasu daga cikin ministocin Najeriya sun yi murabus domin rsayawa takara a matakai daban-daban, lamarin da ya tilasta musu dole su yi murabus sakamakon sabuwar dokar zaɓe da ta yi tanadin haka.