On Air Now

ZANGON BARKA DA SAFIYA

5:00am - 10:00am

Majalissar Dokokin Najeriya Na Shirin Zartar Da Kasafin Kudin 2024 Ranar 23 Ga Watan Disamba 2023

Muddin ba’a samu wani sauyi na gaggawa ba, Majalisar dokoki a Najeriya za ta iya zartar da kasafin kudin 2024 na Naira trilliyan 27.5 a ranar Asabar bayanda ma'aikatu da sassa, da hukumomin tarayya 541 suka kammala  kare bangarorinsu.

Shugaban kwamitin kasafin kudi na majalisar dattawa, Sanata Adeola Solomon, ya shaidawa manema labarai a ranar Litinin cewa majalisar za ta koma zamanta a ranar Laraba.

A cewarsa, kwamitin nasa ya bude sakatariyar sa, inda dukkanin kananan kwamitocin majalisar dattawa za su mika rahotonsu.

Ya bayyana kwarin gwiwar cewa kwamitin kasafin kudi zai gabatar da rahotonsa a ranar Alhamis, inda ya kara da cewa za a zartar da kasafin a ranar Asabar.