On Air Now

ZANGON BARKA DA SAFIYA

5:00am - 10:00am

Majalissar Wakilan Najeriya Ta Bada Umarnin Gayyatar Tsohon Ministan Sufurin Sama Hadi Sirika

Majalisar Wakilai ta umarci kwamitinta kan harkokin sufurin jiragen sama da ya gayyaci tsohon ministan sufurin jiragen sama, Hadi Sirika, domin ya yi mata bayanin halin da kamfanin jirgin sama na kasa, Nigeria Air, ke ciki,  zuwa lokacin da ya bar mulki.

Ana saran tsohon ministan zai bada haske a kan batutuwa da dama da suka shafi aikin.

Hakan ya biyo bayan amincewa da kudirin da Tarkighir Dickson ya gabatar a zauren majalisar a ranar Alhamis.

Da yake gabatar da kudirin, Dickson ya ce gwamnatin da ta shude ta kashe biliyoyin kudade domin samar da sabon kamfanin jirgi na kasa amma har yanzu ba a san matsayin aikin ba.

Idan dai za a iya tunawa a watan Satumba ne Ministan Sufurin Jiragen Sama Festus Keyamo ya dakatar da aikin na Najeriya Air.