On Air Now

Off Air

Midnight - Noon

Mali Ta Sanar Da Lokacin Janyewa Daga Kungiyar G5 Sahel A Cikin Watan Yuni

Wata guda bayan da kasar Mali ta ce za ta janye daga kawancen kungiyar kasashen Sahel, yanzu haka gwamnatin mulkin sojin kasar ta sanar da cewa janyewar za ta fara aiki daga ranar 30 ga watan Yunin nan.

Daga wannan rana ce dakarun Mali da ke  cikin hadakar yaki da ta’addanci a gabashi da tsakiyar kasar, da kuma jami’an sojin Mali da ke aiki a shelkwatar rundunar hadakar za su janye kacokan.

An kafa rundunar yaki da ta’addancin ta yammacin Afrika ne a shekarar 2014 da goyon bayan Faransa, kuma ta kunshi Mauritania, Chadi, Burkina Faso da Nijar.

Dakarun G5 Sahel din na aiki ne a yankuna 3 da suka hada da iyakar Mali da Mauritania, da iyakar Chadi da Nijar da kuma tsakiya da ta hade yakunan kan iyakokin 3.

Mali ta yanke shawarar janyewa daga wannan hadaka ce bayan da aka hana ta shugabantar kungiyar.