On Air Now

Off Air

Midnight - 5:00am

Manchester City Ta Yi Wasan Kura Da Bayern Munich

MANCHESTER CITY

Dan wasa Rodri ya zura wata kwallo ta ban mamaki sannan Erling Haaland ya sake kafa tarihin zura kwallo a raga yayin da Manchester City ta doke Bayern Munich da ci 3 da nema a ranar Talata a kokarinsu na neman lashe gasar zakarun Turai karon farko.

Haaland, wanda ya ci kwallo ta uku da City ta ci a daren a minti na 76, yana da kwallaye 45 a  gasar.

Ayanzu haka dan wasa Erling Haaland yana rike da kambun  tarihin dan wasan Premier da ya fi zura kwallaye a gasar.

Shi kuwa dan wasa Romelu Lukaku ya zura kwallo a  bugun daga kai sai mai tsaron gida a minti na 82, yayin da Inter Milan ta samu damar tsallakewa zuwa matakin kusa da na karshe a gasar cin kofin zakarun Turai bayan ta doke Benfica da ci 2 da nema.